Declane Rice na Arsenal ya ce kawo ƙarshen shekara 14 ba tare da nasara ba a Anfield ya ƙara musu kwarin gwiwar cewa za su iya kare kofin Premier League da suka dauka a bara, amma ya jaddada cewa 'yan wasan ba za su yi murna fiye da kima ba. Nasarar da suka samu da ci 1-0 ba wai kawai ta kawo ƙarshen jiran doke Liverpool a Anfield tun daga 2012 ba, har ma ta mayar da kungiyar kan teburin Premier League, kuma Mikel Arteta ya buga wasan da Gunners ta yi nasara a kan Liverpool a 2012. Yanzu haka Arsenal tana kan teburin Premier League da tazarar maki uku tsakani da Manchester City, wadda ta yi rashin nasara 1-0 a hannun Brighton a karhen mako.